Home Home Mun Kammala Duk Shirye-Shirye Kan Babban Zaɓen 2023, Inji INEC Da ‘Yan...

Mun Kammala Duk Shirye-Shirye Kan Babban Zaɓen 2023, Inji INEC Da ‘Yan Sanda

126
0
Hukumar Zaɓe mai zaman kan ta ta Ƙasa INEC, da rundunonin ‘yan sanda na jihohin Edo da Delta da Bayelsa, sun ce sun kammala duk wani shiri domin gudanar da manyan zaɓuɓɓukan shekara ta 2023 ba tare da cikas ba.

Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe hukumar da ke waɗannan jihohin ne su ka bayyana haka, a wasu hirarraki da su ka yi a lokuta daban-daban da manema labarai.

Sun ce ƙarin hare-haren ta’addanci da ake kai wa ofisoshi da kayan aikin su a faɗin Nijeriya bai sa sun karaya a kan ƙudirin su ba.

Kwamishinan Zaɓe na jihar Delta Monday Udoh-Tom, ya ce sun gama dukkan tsare-tsaren da su ka kamata domin tabbatar da ganin an yi zaɓe cikin lumana.

Ya ce a cikin watanni takwas da su ka gabata, hukumar zaben ta yi gagarumin aikin wayar da kan jama’a, domin tabbatar da ganin an gudanar da sahihin kuma karɓaɓɓe mai cike da adalci.