Home Home Kakakin Majalisa Gbajabiamila, Ya Yi Barazanar Bada Sammacin Kamo Emefiele

Kakakin Majalisa Gbajabiamila, Ya Yi Barazanar Bada Sammacin Kamo Emefiele

145
0
Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar kama Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele.

Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar kama Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele.

Gbajabiamila, ya ce ba zai tsaya ɓata lokaci ba wajen umartar shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Usman Alkali Baba ya buga sammacin kamo Emefiele cikin gaugawa ba.

Kakakin majalisar ya yi barazanar ne, bayan ya karɓi rahoton kwamitin da aka ɗora wa nauyin ganawa da Kwamitin kula da Bankuna da Babban Bankin Nijeriya a karkashin Alhassan Ado Doguwa, inda ya ce Bankin CBN da Emefiele sun ƙi amsa gayyatar bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai a ranar Larabar da ta gabata.

Femi Gbajabiamila, ya ce a shirye ya ke ya yi amfani da Sashe na 89 (1) (d) na Dokar shekara ta1999, wanda ya ba Majalisa ƙarfin ikon umartar jami’an tsaro su kamo mata duk wanda doka ta bada damar a kamo.

Leave a Reply