Muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya mai ɗaurewa a Najeriya idan aka tabbatar masa da muƙamin shugabancin rundunar sojin ƙasa.
Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwaminitin tsaro na majalisar wakilai.
Ya ce matsalar tsaron Najeriya a yanzu na buƙatar haɗin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya a lungu da saƙo na ƙasa.
Ya ce, a sama da shekara 30 da ya yi yana aikin soja, ya yi aiki a wurare daban-daban a rundunar sojin ƙasa na Najeriya,
Don haka ba zai tsame hannun sa daga dukkan nasarori ko rashin sa da aka samu a baya ba,
Amma idan aka tabbatar da shi zai samu wata dama ta jan ragamar rundunar tare da kawo wasu dabarun da za su taimaka domin rundunar ta samu ƙarin nasarori.














































