Dillalan Man Fetur a Najeriya sun ce da yiwuwar farashin litar man fetur ya ragu zuwa tsakanin Naira 900 ko 1,000, a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara bisa yunkurin matatar mai ta Dangote.
Shugaban kungiyar masu sayar da mai a gidajen mai na kasa (PETROAN), Billy Gillis-Harry, da Kakakin kungiyar dillalan mai na kasa (IPMAN), Chinedu Ukadike, suka shelanta haka.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan, Gillis-Harry ya ce rigin farashin da matatar Dangote ta yi zai taimaki ‘yan Nijeriya sosai.
A cewar sa, da yiwuwar farashin ma zai ci gaba da sauka amma ya danganta ne da farashin danyen mai da kuma matatar Dangote.
Wannan matakin na zuwa ne bayan da matatar man Dangote a ranar Lahadi ta rage farashin Litar mai da naira 20, inda ta dawo naira 970 daga naira 990 kan lita guda.
Kamfanin ya yi bayanin cewa an yi hakan ne domin nuna godiya ga goyon bayan ‘yan Nijeriya, wannan kuma na zuwa ne bayan makonni da matatar ta sanya hannu da dillalan mai domin sayar musu da mai kai tsaye.














































