Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya tsakanin 1966 da 1975, janaral Yakubu Gowon, mai murabus ya bayyana damuwa da karuwar matsalar tsaro dake addabar ‘yan Najeriya a bangarorin daban-daban.
Yayin da yake jawabi ga gamayyar ‘yan dimokiradiyyar Arewa karkashin jagorancin Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano,
janar Yakubu Gowon, ya ce yana takaici game da matsalar rashin tsaron Najeriya.
Ya ce yana matukar takaici game da al’amuran dake faruwa a sassan kasa da dama, musamman a yankin Arewa,
Dattijon ya kuma shawarci ‘yan Arewa su zauna lafiya tare da warware matsalolin su cikin lumana.
Ya ce babban abin takaici ne yadda Lakurawa auka karu a jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda dake salwantar da rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriyar musamman mazauna yankin arewa.
Duk da cewa ma’aikatar tsaro ta bayyana cewa ‘yan kungiyar basu hauwar mutum 200 ba, wasu rahotanni na cewa kungiyar na yaduwa zuwa wasu sassan arewa.














































