Home Home Abdulmalik Tanko Ya Musanta Zargin Kashe Hanifa

Abdulmalik Tanko Ya Musanta Zargin Kashe Hanifa

187
0

Abdulmalik Tanko babban wanda ake zargi da sacewa tare da kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar a Kano , ya musanta zargin da aka karanto masa shi da wasu mutum biyu a kotu yayin da ake ci gaba da shari’ar a yau Litinin.

Kazalika, Abdulmalik Tanko da Hashimu sun musanta zargin garkuwa da Hanifa da ba ta guba da kuma binne gawar ta a wata makaranta kamar yadda aka ganu su a bidiyo suna amsawa tun da farko.

Sai dai sun amsa zargi ɗaya cikin uku da aka karanto musu, wanda shi ne na haɗa baki.

Ita ma Fatima, wadda ke cikin waɗanda ake zargin, ta musanta zargin da aka karanto mata na rubuta wasiƙa ga iyayen Hanifa cewa ana buƙatar kuɗin fansa naira miliyan shida a madadin Abdulmalik Tanko.

A zaman da aka yi ranar 7 ga watan Fabarairu waɗanda ake zargin suka nemi gwamnati ta ba su lauyan da zai kare su, aka kuma basu Barista M. L. Usman daga ƙungiyar Legal Aid da Barista P. A. Ademakun su kare su.

Mai Shari’a Sulaiman Na’abba ya ɗage zaman kotun zuwa 2 da 3 ga watan Maris mai zuwa don sauraron shaidu.

Leave a Reply