Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta ayyana shiga yajin aiki na sati huɗu a matsayin gargaɗi ga gwamnatin tarayya.
Shugaban kungiyar ta ASUU Farfesa Emmanuel Victor Osodeke, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Litinin bayan wata ganawa da majalisar zartarwar ƙungiyar ta yi ta tsawon kwana biyu.
Shugaban ƙungiyar reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, a Kano ya ce shugabannin ƙungiyar na jihohoi na kan hanyar su ta komawa don sanar da ƙungiyoyin nasu halin da ake ciki.
Tun a ranar Asabar ne shugabannin ASUU suka fara ganawa a Jami’ar Legas don cimma matsaya kan abin da suka kira saɓa alƙawari na gwamnatin tarayya.
Malaman jami’ar da suka dakatar da aiki tsawon wata tara a 2020, sun sha kokawa kan halin da ilimi ke ciki a Najeriya, ciki har da maganar albashin su.