Home Labaru Matsalar Tsaro: An Rufe Manyan Hanyoyi Da Kasuwannin Wasu Sassan Jihar Katsina

Matsalar Tsaro: An Rufe Manyan Hanyoyi Da Kasuwannin Wasu Sassan Jihar Katsina

53
0

Sakamakon matsalar tsaron da ta addabi Jihar Katsina, Gwamnatin Jihar ta haramta zirga-zirgar ababen hawa a hanyar da ta tashi daga Jibiya zuwa Gurbin Baure har sai abin da hali ya yi.

Dokar ta kuma shawarci duk masu bin hanyar da su yi amfani da hanyar Funtuwa.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sabuwar doka da Gwamnan Jihar, Aminu Bello ya sanya wa hannu ranar Talata.

Kazalika, dokar ta haramta wa motocin haya bin hanyar Kankara zuwa Sheme, amma masu motocin kansu zasu iya bin hanyar.

Gwamnatin ta kuma haramta wa manyan motoci daukar itace daga dukkan dazukan Jihar tare da haramta sayar da dabbobi a kasuwannin Kananan Hukumomin Jibia da Batsari da Safana da Charanchi da Mai’adua da Malumfashi da Kafur da Sabuwa da Kankara da Faskari da Baure da Danmusa da Dutsinma da Kaita.

Dokar dai za ta fara aiki ne daga ranar Talata, 31 ga watan Agustan 2021.

Gwamnatin ta kuma haramta jigilar dabbobi a manyan motoci zuwa sassan kasar nan daga Jihar da kuma daukar mutum uku a kan babur ko kuma sama da mutum uku a motar Kurkura a fadin Jihar.