Home Labaru Ta’aziya: Gwamna Zulum Ya Nemi Afuwar Iyalan Faston Da Aka Harbe A...

Ta’aziya: Gwamna Zulum Ya Nemi Afuwar Iyalan Faston Da Aka Harbe A Maiduguri

58
0
     Ta’aziya: Gwamna Zulum Ya Nemi Afuwar Iyalan Faston Da Aka Harbe A Maiduguri

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ziyarci gidan Fasto Bitrus Tumba wanda ya mutu a lokacin wani rikici da ya kaure tsakanin jami’an hukumar tsara birane ta jihar, BOGIS da wasu Kiristocin da ke bauta a cocin EYN da ke birnin Maiduguri.

Zulum ya nemi afuwar iyalan marigayin tare da jaddada cewa ana binciken yadda lamarin ya auku kuma za su yi kokari wajen ganin sun yi adalci.

Gwamnan ya ce kowanne ɗan Borno na da ƴanci domin haka ba za su lamunci tauye hakki ko cin zarafin kowanne mutum ba.

Matakan da gwamnati ta dauka na rusa wasu gine-gine da ake ganin ba bisa tsari suke ba ya haifar da kazamin rikici da tayar da hankula a wasu yankunan Maiduguri.