Home Labaru Ilimi Gurbin Karatu: JAMB Ta Soke Mafi Karancin Makin Shiga Manyan Makarantu Na...

Gurbin Karatu: JAMB Ta Soke Mafi Karancin Makin Shiga Manyan Makarantu Na Bana

113
0

Hukumar tsara jarabawar shiga Manyan Makarantu ta Najeriya wato JAMB ta soke mafi karancin makin da za a bukaci dalibai su samu kafin a basu gurbin karatu a manyan makarantun.

Hakan dai na nufin yanzu hukumar ta ba makarantun wuka da nama wajen yanke yawan makin da kowaccen su take bukata ga dalibi kafin ta ba shi gurbin karatun a cikin ta.

Hukumar dai ta dauki matakin ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki na 2021 da ya gudana ta intanet ranar Talatar nan.

Taron ya gudana ne karkashin jagorancin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu.