Home Labaru Ta’addanci: ‘Yar Kunar Bakin Wake Ta Kashe Mutum 6 A Chadi

Ta’addanci: ‘Yar Kunar Bakin Wake Ta Kashe Mutum 6 A Chadi

242
0

Wata ‘yar kunar bakin wake ta kai hari a yammacin kasar Chadi, inda ta salwantar da rayukan mutane shida, yayin da ta tayar da bam din da ke jikinta.

Ana zargin cewar kungiyar Boko Haram ne ta kai wannan mummunan hari, inda mutane shida suka rasa rayukansu, wandada  da suka hada da wani soja guda daya a gundumar Kaiga-Kindjiria.

Wani jami’in tsaro a gundumar Kaiga ya ce, macen ‘yan kunar bakin wake ta shi da bam din da ta dauro shi a jikinta kusa da fadar wata masarautar gargajiya.

Dogarai hudu da kuma wani jami’in soja guda daya, na cikin mutane 6 da suka riga mu gidan gaskiya, yayin da mutane 5 suka jikkata.

Kakakin rundunar sojin kasa na kasar Chadi, Kanal Azem Bermandoa, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan harin.

Gundumar Kaiga wani babban yanki ne a gabar tafkin Chadi da ke iyaka da kasar Kamaru, Chadi, Nijar da kuma Najeriya.