Home Home Makomar Ramaphosa: Jam’Iyyar ANC Na Tattaunawa Kan Shugaban Afirka Ta Kudu

Makomar Ramaphosa: Jam’Iyyar ANC Na Tattaunawa Kan Shugaban Afirka Ta Kudu

31
0
South African Deputy-President Cyril Ramaphosa speaks during a rally to commemorate Nelson Mandela's centenary year in Cape Town, South Africa, February 11, 2018. REUTERS/Mike Hutchings

Babban kwamitin jam’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu zai gana da mambobinsa a yau Litinin, domin tattauna makomar shugaban kasar Cyril Ramaphosa.

Wani rahoto da aka fitar ya zargi Mr Ramaphosa, da aikata ba daidai ba, da yiwuwar take dokokin ofishinsa.

Ana zargin ya boye tsabar miliyoyin daloli a gidan gonarsa, ba tare da ya sanar da bacewarsu ba a lokacin da aka sace kudaden.

A jawabin da ya yi a jiya Lahadi, shugaban na Afirka ta Kudu, ya ce makomarsa ta ta’allaka ne a hannun ‘yan jam’iyyarsa.

Wannan danbarwa dai ta janyo an fara tababar ko jam’iyyar ANC za ta sake tsaida shi a matsayin shugabanta a babban taron da za su yi a karshen watan nan.