Home Home Dubu Ta Cika: NDLEA Ta Kama Mai Tsohon Ciki Dauke Da Tabar...

Dubu Ta Cika: NDLEA Ta Kama Mai Tsohon Ciki Dauke Da Tabar Wiwi a Rivers

35
0

Hukumar hana sha da fataucin ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wata mata mai juna-biyu ɗauke da ganyen wiwi mai nauyinsa kilogiram 34.3.

An kama matar ƴar shekara 29 ne a yankin Okrika na jihar Rivers.

Sai dai shugaban hukumar, Birgediya janar Buba Marwa mai murabus ya umurci a bayar da belin matar har sai ta haihu, kasancewar cikin nata ya kai wata tara.

Wata sanarwar da NDLEA ta fitar ta hannun babban jami’in hulda da jama’a na hukumar Femi Babafemi ta ce an kama wata tsohuwa mai shekara 60 a jihar Oyo da ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 5.5.

Toshuwar ta yi bayanin cewa ganyen wanda aka ɓoye a cikin lasifika, ya fito ne daga wurin wata ƴarta da ke zaune a Afirka da kudun.