Majalisar dattawa ta ƙi amincewa da kasafin shekara ta 2023 da ta shirya amincewa da shi yayin zaman ta na ranar Alhamis din nan.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce rashin amincewa da kasfain ya biyo bayan kura-kuran da kasafin ke kunshe shi daga banagren gwamanti.
Ya ce Sakamakon wasu ƙalubale, ba za su iya karbar rahoton kwamitin kula da kasafi na majalisar ba saboda ya je ma su da matsaloli.
Sanata Ahmed Lawan, ya ce sai a ranar Larabar da ta gabata ne majalisar ta sake karɓar ƙarin wasu buƙatu daga shugaban kasa na kari a kasafin domin wasu ayyukan musamman na naira tirilliyan 23 da biliyan 700.
Ya ce sun tsaida Laraba 28 ga watan Disamba na shekara ta 2023 a matsayin ranar da za su amince da kasafin.














































