Home Home makarantar firamare mai malamai 2 kacal da adadin dalibai 544 a jihar...

makarantar firamare mai malamai 2 kacal da adadin dalibai 544 a jihar yobe

43
0
Duk da yawan ikirarin da gwamnatin jihar Yobe ta sha yi na inganta harkokin ilimi, yanzu haka an gano wata makarantar firamare da ke kauyen Ngelshengele a karamar hukumar Fune, wadda ke da malamai biyu kacal tare da adadin dalibai 544 a makarantar.

Shugaban makarantar Malam Sa’id Wakil, ya koka dangane da rashin malamai a makarantar, lamarin da ya ce ya na daya daga cikin manyan kalubalen da makarantar ke fuskanta.

Ya ce akwai wani malami daya da aka tura zuwa makarantar, amma sun gano cewa dalibi ne daga Gashuwa.

Malam Sa’id ya kara da cewa, baya ga rashin malamai, kusan dukkan ajujuwan makarantar su na bukatar gyara.