Home Home Peter Obi Ya Bayyana Manufofinsa

Peter Obi Ya Bayyana Manufofinsa

36
0
Ɗan takarar Shugaban kas na Jam'iyyar Labour Peter Obi, ya bayyana ƙudurorin da zai maida hankali a kan su idan ya samu nasarar lashen zaɓen shekara ta 2023.

Ɗan takarar Shugaban kas na Jam’iyyar Labour Peter Obi, ya bayyana ƙudurorin da zai maida hankali a kan su idan ya samu nasarar lashen zaɓen shekara ta 2023.

Mista Obi dai ya bayyana ƙudurorin nasa mai shafuka 72 a shafin sa na Tuwita, inda ya lissafo batutuwa bakwai da ya ce gwamnatin shi za ta maida hankali a kan su idan aka zaɓen shi a matsayin shugaban ƙasa.

Ƙudurorin dai sun haɗa da kawo ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga, da masu tada ƙayar baya, da kuma kawo gagarumin sauyi a fannin shari’a ta yadda doka za ta yi aiki a kan kowa.

Haka kuma, daga cikin manufofin nasa, Peter Obi ya ce zai gina manyan abubuwan more rayuwa na zamani domin samar da wadatacciyar wutar lantarki, sannan ya yi alƙawarin bunƙasa fannin sufurin jiragen ƙasa da na sama da kuma titunan mota.