
Helkwatar Tsaro ta Nijeriya, ta zargi kamfanin dillancin labarai na Birtaniya, Reuters, da kokarin bata sunan Rundunar Sojin Nijeriya ta salon aikin jarida.
Daraktan yada labarai na helkwatar Manjo Janar Jimmy Akpor ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Manjo Janar Jimmy Akpo,r ya ce Reuters ta ayyana shirya wasu jerin rahotani a kan abin ya kira yakin da rundunar sojin ke yi da ‘yan ta’addar da ke yaki da sunan Musulunci a yankin Arewa maso Gabas tsawon shekaru 13.
Sanarwar ta ce, shirin kamfanin dillancin labaran zai maida hankali a kan abin da ya kira aikin zubar da ciki na dole ga matan da ‘yan ta’addan su ka yi wa ciki, da kuma wani shiri na kisan yara kanana da ta ce sojojin ke yi a wani mataki na dakile ta’addanci.
Tuni dai daraktan ya karyata wadannan zarge-zargen da kuma kage, ya na mai cewa wannan abin da kafar yada labaran ke shirin yi tsagwaron mugunta ce da kuma bata suna ta hanyar amfani da aikin jarida.













































