Majalisar dattawa ta ce za ta ci-gaba da biyan Sanata Orji Uzor Kalu albashi da alawus-alawus din sa, duk da cewa kotu ta yanke masa hukuncin zaman shekaru 12 a gidan yari.
Mai magana da yawun majalisar Sanata Godiya Akwashiki ya bayyana haka ga manema labarai, tare da cewa za a biya Orji Kalu dukkan hakkokin sa saboda har yanzu shin sanata ne.
Akwashiki ya kara da cewa, majalisaza ta cigaba da ba Kalu matsayin san a sanata har sai lokacin da kotun koli ta yanke hukuncin kwace kujerar sa. Kawo yanzu dai sa nata Orji Uzor Kalu ya na kurkuku, sai dai lauyoyin sa na shirin komawa kotu domin bada beli.
You must log in to post a comment.