Home Labaru Gwamna Ganduje Ya Nada Muhammadu Sanusi II Shugaban Sarakunan

Gwamna Ganduje Ya Nada Muhammadu Sanusi II Shugaban Sarakunan

362
0
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zabi mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin wanda zai jagoranci majalisar Sarakuna na jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamna Ganduje ya nada Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Shugaban Sarakunan ne jim kadan bayan kafa wasu sababbin Masarautu a jihar.

Mai Magana da yawun gwamnan Abba Anwar, ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar, inda ya ce, nadin ya dogara ne bisa sashe na 4(2) da sashe na 5(1) (2) na dokokin masarautar.

Anwar ya kara da cewa, dokar da aka sa wa hannu a shekara ta 2019, gwamna Ganduje na da damar nada Sarkin da zai sauran sarakunan da ke karkashin majalisar sarakuna ta jihar.

Sarakunan da aka nada sun hada da Dr Tafida Abubakar a matsayin sarkin Rano, sai Ibrahim Abdulkadir a matsayin Sarkin Gaya, sai  Ibrahim Abubakar II Sarkin Karaye, wanda dukkakin nade-naden sun fara aiki daga ranar Litinin din nan 9 ga Watan Dimsaban 2019.