Home Labaru Dole Malaman Jami’o’i Su Shiga Tsarin IPPIS – Buhari

Dole Malaman Jami’o’i Su Shiga Tsarin IPPIS – Buhari

403
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya zama dole ma’aikatan jami’o’i su shiga tsarin biyan albashi na IPPIS domin tabbatar da gaskiya wajen biyan ma’aikatan.

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin sakataren hukumar TETFund mai kula da cigaban makarantun gaba da sakandare a wajen taron yaye daliban jami’ar Jos.

Farfesa Suleiman Elias Bogoro da uya gabatar da jawabi a madadin shugaban kasa muhammdu Buhari, ya bayyana fa’idar shiga tsarin biyan albashi na IPPIS, tare da cewa tsarin zai taimaka wajen kashe kudi ke-ke-da-ke.

Bogoro ya kara da cewam tsarin IPPIS na cikin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo rashin gaskiya a manyan makarantu na gaba da sakandare da ke fadin Nijeriya.

Farfesa Bogoro wanda ya kasance a matsayin babban bako a wajen bikin yaye daliban jami’ar JOS ya shawarci jam’o’i kasar’nan su kara kokarin wajen inganta harkokin ilmi ta yadda daliban Nijeriya za su iya shiga ko ina a Duniya.

Gwamnatin tarayya dai ta ce dole ne ma’aikatan jami’o’i sun shiga tsarin biyan albashi na IPPIS ko kuma a dakatar da albashin su.

Sai dai a na ta bangaren, kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta ce ba zata amince da hakan ba, ta karyata ikirarin gwamnatin tarayya cewa ma’aikata dubu 39 sun shiga IPPIS.