Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Majalisar Dattawa Ta Ce Za Ta Cigaba Da Biyan Orji Uzor Kalu Albashi

Sanata Orji Uzor Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu

Majalisar dattawa ta ce za ta ci-gaba da biyan Sanata Orji Uzor Kalu albashi da alawus-alawus din sa, duk da cewa kotu ta yanke masa hukuncin zaman shekaru 12 a gidan yari.

Mai magana da yawun majalisar Sanata Godiya Akwashiki ya bayyana haka ga manema labarai, tare da cewa za a biya Orji Kalu dukkan hakkokin sa saboda har yanzu shin sanata ne.

Akwashiki ya kara da cewa, majalisaza ta cigaba da ba Kalu matsayin san a sanata har sai lokacin da kotun koli ta yanke hukuncin kwace kujerar sa. Kawo yanzu dai  sa nata Orji Uzor Kalu ya na kurkuku, sai dai lauyoyin sa na  shirin komawa kotu domin bada beli.

Exit mobile version