Home Labaru Majalisa Ta Umarci Hukumar Kwastan Ta Biya Diyyar Naira Miliyan 360

Majalisa Ta Umarci Hukumar Kwastan Ta Biya Diyyar Naira Miliyan 360

283
0

Majalisar wakilai ta amince da rahoton kwamitin da ya umarci Hukumar Kwastam ta biya diyyar Naira miliyan 360 ga iyalan mutane 18 da jami’an ta su ka kashe a jihohin Katsina da Oyo.

Haka kuma, majalisar ta bukaci a gurfanar da dukkan jami’an hukumar da ke da hannu a kisan domin a hukunta su.

Daga cikin kuɗaɗen dai, za a biya Naira miliyan 200 ga iyalan mutane 10 da jami’an kwastam su ka kashe a garin Jibiya na Jihar Katsina, yayin da ta umarci a biya diyyar Naira miliyan 160 ga mutane 8 da aka kashe a Jihar Oyo.

Majalisar ta dauki matakin ne, bayan kwamitin kula da harkokin fasa-kwauri ya bada sakamakon binciken da ya gudanar.

Mataimakin Shugaban Majalisar wakilai Idris Wase ya jagoranci zaman, ya kuma amince da rahoton da Shugaban Kwamitin Kwastan Leke Abejide ya gabatar.

Leave a Reply