Home Labaru Buhari Ya Yi Magana Da Shugaban Kasar Da Aka Yi Yunkurin Kifar...

Buhari Ya Yi Magana Da Shugaban Kasar Da Aka Yi Yunkurin Kifar Da Gwamnatin Sa

150
0
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci a kan rikicin shugabanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar APC.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya yi magana da takwaran sa na kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo da sojoji su ka yi yunkurin hambarar da gwamnatin sa.

A wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Shugaba Buhari ya ce ya yi matukar farin ciki da na jin cewa an shawo kan matsalar, kuma al’amura sun koma daidai a kasar.

Buhari ya kara da cewa, ya taya Umaro Sissoco murnar tsallake juyin mulkin, sannan ya yaba wa dakarun kasar masu biyayya da kishin kasa, lamarin da ya ce ya kai su ga samun nasara a kan sojojin da su ka yi tawaye.

Shugaba Buhari, ya ce yunkurin juyin mulkin a Guinea Bissau abu ne da za a yi Allah-Wadai da shi, sannan ya yi alkawarin cewa ‘yan kasar da gwamnatin Embalo za su cigaba da cin moriya da kuma samun goyon bayan gwamnati da al’ummar Nijeriya.

Leave a Reply