Home Labaru An Ceto ‘Yan Matan Nijeriya Daga Hannun Wata Mata A India

An Ceto ‘Yan Matan Nijeriya Daga Hannun Wata Mata A India

59
0

Hukumar yaki da safarar Bil-Adama ta Nijeriya NAPTIP, ta ce jami’an ta tare da hadin gwiwar ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya da ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin New Delhi a kasar Indiya, da kuma ‘yan sandan birnin sun kwato wasu mata da aka yi safarar su daga Nijeriya.

A wata sanarwa da hukumar ta raba wa manema labarai, ta ce matar mai safarar mutane ta kasa da kasa mai suna Joy Shandy Okah ‘yar Nijeriya ce, kuma an kama ta ne a birnin New Delhi, inda aka ceto wasu yara mata guda uku da ta kai su kasar Indiyan tare da tilasta masu yin karuwanci.

Hukumar ta ce kafin dauko su daga Nijeriya, sai da matar ta sa ‘yan matan su ka yi rantsuwa kafin ta kai su kasar India, bayan sun isa can kuma ta kwace wayoyin salular su da takardun bulaguron su.

Matar ta tilasta wa ‘yan matan, wadanda aka tabbabar sahihancin takardun bulaguron su ‘yan asalin jihohin Cross Rivers da Edo, kuma kowace yarinya ta na biyan ta Naira miliyan hudu da dubu dari biyar ta hanyar yin karuwanci.

Tuni dai ‘yan sandan birnin Delhi sun kammala bincike nan take, inda kasa da sa’o’i 24 aka gurfanar da ita gaban kotu domin fuskantar shari’a.