Majalisar wakilai ta amince da rahoton kwamitin da ya umarci Hukumar Kwastam ta biya diyyar Naira miliyan 360 ga iyalan mutane 18 da jami’an ta su ka kashe a jihohin Katsina da Oyo.
Haka kuma, majalisar ta bukaci a gurfanar da dukkan jami’an hukumar da ke da hannu a kisan domin a hukunta su.
Daga cikin kuɗaɗen dai, za a biya Naira miliyan 200 ga iyalan mutane 10 da jami’an kwastam su ka kashe a garin Jibiya na Jihar Katsina, yayin da ta umarci a biya diyyar Naira miliyan 160 ga mutane 8 da aka kashe a Jihar Oyo.
Majalisar ta dauki matakin ne, bayan kwamitin kula da harkokin fasa-kwauri ya bada sakamakon binciken da ya gudanar.
Mataimakin Shugaban Majalisar wakilai Idris Wase ya jagoranci zaman, ya kuma amince da rahoton da Shugaban Kwamitin Kwastan Leke Abejide ya gabatar.

