Home Labaru Kasuwanci Mafita: Ya Kamata Matasa Su Rungumi Nomi Kafin Su Shiga Siyasa –...

Mafita: Ya Kamata Matasa Su Rungumi Nomi Kafin Su Shiga Siyasa – Minista

384
0
Audu Ogbe, Ministan Noma Da Raya Karkara
Audu Ogbe, Ministan Noma Da Raya Karkara

Ministan Noma da raya Karkara Audu Ogbe, ya shawarci matasa su karfafa zuciyoyin su wajen rungumar noma gadan-gadan kafin su fara gaganiyar shiga harkokin siyasa.

Audu Ogbe ya bada shawarar ne a Abuja, yayin da ya halarci taron rattaba hannu a kan yarjejeniya tsakanin kamfanin NAMEL da kuma MANTRAC Nigeria Limited.

An dai kulla yarjejeniyar ne tsakanin kamfanonin biyu domin sama wa matasa filin noma har kadada 500,000 da za a yi amfani da ita wajen bunkasa samar da abinci a Nijeriya. Ministan ya ce, ya kamata matasa su yi karatun ta-natsu, su fahimci cewa nauyin wadatar da Nijeriya da abinci ya rataya ne a wuyan su ba a wuyan kananan yara ko tsofaffi ba.