Kotun Sauraren Kararrrakin Zabe a jihar Kano, ta ce an shigar da kararraki 33 a gaban ta, wadanda duk tankiya ce a kan zabubbukan shekara ta 2019 da aka gudanar.
Shugaban Kotun Mai Shari’a Nayai Aganaba ya bayyana haka, a lokacin da ake kaddamar da zaman kotun a ranar Alhamis da ta gabata a Kano.
Ya ce duk kararrakin da aka karba 33 na zabubbukan Majalisar Dokoki ne da kuma na Majalisar Tarayya, kuma har zuwa ranar Alhamis ba a kai ga shigar da kara a kan zaben gwamna ba.
Anagaba, ya roki jam’iyyun da ke cikin rigingimun shari’ar zabe su ba kotu hadin kai, domin a tabbatar da an gudanar da dukkan yanke hukunci a cikin kwanaki 180 da aka gindaya wa kotun.
Alkalin ya kuma yi alkawarin cewa, kotun za ta yi adalci, kuma ba za ta yi nuku-nuku ko nuna bangaranci wajen yanke hukunci ba.Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano Ibrahim Muktar, ya tattabar wa alkalan cewa za a ba su wadatattun jami’an tsaro da wurin da za su gudanar za zaman shari’a ba tare da fuskantar wata barazana ba.