Ministan Noma da raya Karkara Audu Ogbe, ya shawarci matasa su karfafa zuciyoyin su wajen rungumar noma gadan-gadan kafin su fara gaganiyar shiga harkokin siyasa.
Audu Ogbe ya bada shawarar ne a Abuja, yayin da ya halarci taron rattaba hannu a kan yarjejeniya tsakanin kamfanin NAMEL da kuma MANTRAC Nigeria Limited.
An dai kulla yarjejeniyar ne tsakanin kamfanonin biyu domin sama wa matasa filin noma har kadada 500,000 da za a yi amfani da ita wajen bunkasa samar da abinci a Nijeriya. Ministan ya ce, ya kamata matasa su yi karatun ta-natsu, su fahimci cewa nauyin wadatar da Nijeriya da abinci ya rataya ne a wuyan su ba a wuyan kananan yara ko tsofaffi ba.