Kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamna da ‘yan majalisar dokoki da aka kafa a birnin Gusau na jihar Zamfara, ta koma Abuja saboda dalilai na tsaro kamar yadda kotun ta sanar.
Sakataren kotun Barista Innocent Akidi ya sanar da haka, yayin zaman farko da kotun ta yi a unguwar Wuse da ke Abuja, inda ya ce akwai korafe-korafe akalla 40 da kotun ta karba daga ‘yan takara daban-daban.
Mai shari’a Binta Fatima Zubairu ce ke jagorantar kotun, yayin da Okey I. Nwamoh da A. Y Ajanaku ke manyan alkalan kotun.
A zaman ta na farko a Abuja, kotun ta amince da yin wasu ‘yan sauye-sauye a karar da aka shigar a kan hukumar zabe da jam’iyyar APC da sabon zababben gwamnan jihar Zamfara Idris Mukhtar Shehu. Jam’iyyar PDP da dan takararta Muhammed Bello Matawalle ne su ka shigar da korafin farko a kan wadanda ake kara, yayin da jam’iyyar APGA da dan takarar ta na gwamna Sani Abdullahi Shinkafi su ka shigar da kara ta biyu.
You must log in to post a comment.