Home Labaru Mafi Karancin Albashi: Gwamnati Da Kungiyar Kwadago Za Su Koma Tattaunawa A...

Mafi Karancin Albashi: Gwamnati Da Kungiyar Kwadago Za Su Koma Tattaunawa A Laraba

670
0

Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago za su sake yin zaman tattaunawa a ranar Laraba mai zuwa bayan kwashe watanni 2 ba tare da cimma matsaya ba akan batun kaddamar da sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata tun bayan zaman da suka yi a ranar 27 ga watan Yuli.

mataimakin shugaban kungiyar kwadago

Daya daga cikin dan tawagar tattaunawa wanda shine mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa Amaechi Lawerence ya tabbatar da haka.

Ya ce ya na fata tawagar gwamnatin tarayya za ta gabatar da wasu tsare-tsare da kungiyar za ta gamsu dan ganin ma’aikatan sun fara amfana da alkawarin da aka musu.

Lawerence ya kara da cewa ba a cimma matsaya ba a tattaunawar da bangarorin biyu suka yi ranar  27 ga watan Yuli, bayan da bangaren kungiyar kwadago ya bukaci tawagar gwamnati da ya koma ya kara tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan za a iya tunawa a makon da ya biyo bayan sakamakon rashin cimma matsaya kungiyar TUC ta fara barazanar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.