Home Labaru Rikicin Kabilanci: An Kashe Mutane Da Dama A Taraba

Rikicin Kabilanci: An Kashe Mutane Da Dama A Taraba

569
0

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kai hari wani gari dake jihar Taraba inda suka kashe mutane 15 tare da jikkata wasu da dama.

Wasu mazauna garin sunyi zargin cewa harin ya fito ne daga jihar Benue, a ci gaba da rikice-rikicen kabilanci na kabilar Jukun da Tiv a jihohin 2.

Ya ce maharani sun diram ma garin ne inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi, wanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, baya ga wasu sun tsere.

Wani jami’in tsaron sa kai ya tabbatarwa manema labarai cewa wasu daga cikin maharani wanda sun haura 20 sun yadda makamansu a lokacin da aka korasu wani daji dake kusa da garin.

Ya ce ‘yan ta’addan sun shiga garin ne ta tsaunin Angwan Abakwa da kuma hanyar Wukari.

A nasa bangaren mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, ya ce za a fitar da adadin yawan mutanen da suka rasa rayukansu, da zarar an kammala duba wadanda suka jikkata a Asibiti.