Home Labaru Wutar Lantarki: Gwamanatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Tashar Kashimbilla Dake Taraba

Wutar Lantarki: Gwamanatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Tashar Kashimbilla Dake Taraba

759
0

Gwamnatin tarayya ta ce nan gaba kadan za ta kaddamar da tashar samar da wutar lantarki ta Kashimbilla, dake Takum, Wukari a jihar Taraba domin kara bunkasa wutar lantarki a fadin Najeriya.

Sale Mamman Ministan wutar lantarki

Ministan wutar lantarki Sale Mamman ya tabbatar da haka a lokacin da ya je ziyarar gani da ido tare da karamin ministan wutar lantarki Goddy Agba.

Babban jami’in kula da aikace-aikace na ma’aikatar wutar lantarkin Ali Dapshima Abubakar, wanda ya zaga dasu ya ce an kara inganta aikin da aka yi dan samar da megawatt 6 na lantarki zuwa 40.

A nasa bangaren babban daraktan kamfanin rarraba wutar lantarki ta Najeriya TCN Usman Gur Mohammed ya ce ya gamsu matuka da aikin kammala tashar ta Kashimbila.

Ya ce da zarar tashar ta fara aiki za ta ba yankin Arewa maso gabas, Arewa ta tsakiya da kuma kudu maso gabashin Najeriya wutar lantarki da ake bukata.