Home Labaru Ma’aikatan Filato Sun Fara Yajin Aiki Kan Rashin Biyan Su Albashi

Ma’aikatan Filato Sun Fara Yajin Aiki Kan Rashin Biyan Su Albashi

306
0

Ma’aikatan Jihar Filato sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani,
bayan gwamnatin jihar ta kasa biya masu bukatun su.

An dai ayyana matakin ne a cikin sanarwar yajin aikin da kungiyar hadin gwiwa ta ma’aikjata JNC reshen Filato ta fitar, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Titus Malau da Sakataren ta Timothy Gopep, inda ta ce yajin aikin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da aka gindaya.

Sun ce majalisar ta gudanar da taro tare da shugaban ma’aikatan gwamnati da sakataren gwamnatin jihar Filato, inda su ka ce gwamnati ba ta nuna isasshen kudurin magance matsalolin ba kamar yadda aka gabatar a cikin kundin su na bukatu kafin wa’adin ya kare.

Ma’aikatan sun ce, bayan ganawar hadin gwiwa da shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, an yanke shawarar cewa za a shiga yajin aikin, inda su ka ce matakin ya zama wajibi tun da gwamnati ta yi watsi da nata bangaren na yarjejeniyar duk da alkawurran da ta dauka.

Leave a Reply