Home Labaru Bola Tinubu Ya Taya Gwamnan PDP Murnar Samun Nasara A Kotu

Bola Tinubu Ya Taya Gwamnan PDP Murnar Samun Nasara A Kotu

289
0

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya aike da
saƙon taya murna ga gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun
a kan nasarar da ya samu a kotun ƙoli.

A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun sa Tunde Rahman ya fitar, Tinubu ya buƙaci gwamnan ya yi ƙoƙarin haɗa kan al’ummar jihar da gaugawa.

Tinubu ya ce kotun ƙoli ta kawo ƙarshen tirka-tirkar da ta fara tun daga kan zaɓen gwamnan jihar na watan Yulin shekara ta 2022, inda ya ce dole ne kowane ɓangare ya mutunta hukuncin kotun ƙoli.

Haka kuma, Tinubu ya yaba wa gwamnan jihar da ya sauka Gboyega Oyetola, bisa yadda ya sauke nauyin da ke kan sa cikin aminci a lokacin mulkin sa na farko.

Ya ce tsohon gwamnan ya ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar nan, ta hanyar da ya nemi haƙƙin sa cikin kwanciyar hankali tun daga farko har zuwa ƙarshe.

Leave a Reply