Wani Rahoton shekara ta 2022 da Ofishin kula da basussuka
na kasa ya fitar ya nuna cewa, jimlar bashin da ake bin
Nijeriya a wannan lokacin ya haura Naira Triliyan 46 da
Biliyan 25.
Yayin da ake kirga ‘yan kwanaki Gwamnatin Shugaba Buhari ta nade komatsan ta daga gidan gwamnati, an gano cewa Gwamnati mai jiran gado za ta gaji yawan basussukan da ake bin Nijeriya da ya haura sama da Naira triliyan 80.
Jimlar dai ta hada da wasu kudade da Majalisar Dattawa ta amince da kashe su cikin shekaru 10 da su ka gabata, wadanda aka yi wa lakabi da ‘Ways & Means’ a turance.
Masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu, ya ce basussukan da Nijeriya ta ciwo a cikin shekaru 10, sun fi ta’azara ne a cikin shekaru takwas da su ka gabata, sakamakon cewa kasafin kudin da ake yi ya na da fadi, wanda a shekara ta 2022 da 2023 kasafin kudin da aka yi ya kai kusan naira triliyan 20.














































