Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala aikin tashar samar da wutar lantarki ta Kashimbilla mai karfin megawati 40 wadda dake Wukari ta jihar Taraba.

Ministan wutar lantarki, Injiniya Sale Mamman, ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ziyarci wurin da aikin ke gudana tare da karamin ministan wutar lantarki Goddy Agba da wasu jigajigan ma’aikatar tasu.
Haka zalika sun ziyarci sauran bangarorin da irin wadannan ayyukan ke gudana a Takun inda ake sa wasu na’urorin samar da lantarkin masu karfin megawatt 60.
Anashi bangaren babban Manajan dake kula da ayyukan, Injiniya Ali-Dapshima Abubakar, ya ce aikin tashar ta Kashimbilla ta samu kari daga megawatt 6 zuwa 40 a halin yanzu.
Ya kara da cewa an fara
aikin dam din ne tun a watan Oktobar 2017, a yanzu haka aiki na daf da kaiwa
karshe ya na mai cewa nan ba da jimawa ba tashar za ta soma aiki.
You must log in to post a comment.