Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sallami daya daga cikin masu bashi shawara na musamman a kan harkokin siyasa, Musa Shittu, bayan makonni shida da nada shi.
Sanar sallamar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ladan Salihu, ya fitar, inda sanarwar ta ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take ba tare bayyana da dalilan daukan makin yin hakan ba.
Gwamnan jihar ya yi godiya ga tsohon mai bashi shawarar da irin gudummawar da ya bayar domin ci gaban jihar inda kuma yayi masa fatan alheri a gaba.
You must log in to post a comment.