Home Labaru Samar Da Ayyuka: Gwamnatin Tarayya Ta Jaddada Kudurinta

Samar Da Ayyuka: Gwamnatin Tarayya Ta Jaddada Kudurinta

234
0
Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta jaddada kudurinta na inganta shirye-shirye da tsare-tsare na samar da ayyukan yi a fadin Najeriya.

Babban jami’in shirin rage zaman kashe wando da inganta rayuwa ta hanyar zuba jari Justice Bibiye ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Bibiye ya ce mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin samar da ayyukan yi Afolabi Imoukhuede ya bayyana haka a lokacin kaddamar da hekta 40 na noma karkashin shirin noma na N-Power a Kwara.

Ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta samarwa matasa da dama aiki ta hanyar kirkiro da tsare-tsare, wanda a baya basu samu irin wannan damar ba.