Rundunar ‘yan sandan ta ce ta kama wasu mutum 130 bisa zargin laifukan da suka shafi laifukan intanet.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce daga cikin mutanen da ta kama, mutum 113 ‘yan ƙasashen China da Malaysia ne.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kama mutanen – ciki har da ‘yan Najeriya 17 – a wani gini da ke unguwar Jahi a Abuja, babban birnin ƙasar.
”Mutanen na amfani da kwamfutoci da wasu na’urori wajen aikata laifukan,
‘Yansanda sun kuma ce suna gudanar da bincike game da mutanen, tare da yi zuzzurfan nazari kan abubuwan da aka ƙwato a wajensu, kafin a gabatar da su a gaban kotu.














































