Home Labarai Rikicin Siyasa: Baraka Ta Kunno Kai A Kwankwasiyya

Rikicin Siyasa: Baraka Ta Kunno Kai A Kwankwasiyya

48
0
Sani Madakin Gini
Sani Madakin Gini

Babbar ɓaraka ta kunno kai a tafiyar siyasar Kwankwasiyya ta jam’iyyar NNPP, yayin da ‘yan majalisar tarayya biyu a jihar suka sanar da ficewa daga tafiyar.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai ta kasa Ali Sani Madakin Gini ya tabbatar da cewa ya fita daga tsagin Kwankwasiyya a cikin jam’iyyarsa ta NNPP.

Haka shi ma takwaransa da ke wakiltar ƙananan hukumomin Kibiya da Rano da kuma Bunkure, Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya sanar da raba gari da tafiyar ta kwankwasiyya.

Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano, wanda jam’iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun.

A kwanan baya ne dai wata ƙungiya ta ɓullo a fagen siyasar Kano mai taken ‘Abba Tsaya da Ƙafarka’ mai rajin gwamnan na Kano ya daina biyayya ga jagoran Kwankwasiyya, ya ci gashin kansa.

lamarin da ya janyo jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da wani kwamishina, bisa zarginsu da alaƙa da ƙungiyar.

Leave a Reply