Home Labarai Fifita Yarbawa: Kungiyar AFENIFERE Ta Soki Lamarin Shugaban Kasa Tinubu

Fifita Yarbawa: Kungiyar AFENIFERE Ta Soki Lamarin Shugaban Kasa Tinubu

48
0
download (23)
download (23)

Ƙungiyar kishin ƙabilar Yarabawa zalla ta Afenifere ta gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan abin da ta kira sonkai da fifita ‘yan ƙabilar Yarabawa wajen bayar da muƙaman tarayya.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Ayo Adebanjo, da kuma sakatarenta na yaɗa labarai Justice Faleye suka fitar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa lamarin zai iya zama barazana ga alaƙar ƙabilu da kuma zaman tare na lumana a tsakanin ƙabilun ƙasar.

Afeniferen ta kuma jaddada buƙatar ganin shugaban ya gyara kuskuren da ta tace ya yi a kan bayar da muƙaman.

A sanarwar ƙungiyar ta ce ba za ta taɓa lamunta da tsabar sonkai da nuna bambanci da Tinubu yake yi ba inda ya naɗa Yarabawa shugabannin dukkanin hukumomin yaƙi da miyagun laifuka da kuma tattalin arziƙi ba.

Afeniferen ta ce ba ta yadda za ta yi shekara da shekaru tana yaƙar abin da ta kira kaka-gida na mulkin Fulani, sannan kuma yanzu ta goyi bayan kaka-gida na Yarabawa ko wata ƙabila ba.

Leave a Reply