Home Labaru Kwatsam Ta Zayyana Ƙa’Idoji Kafin Fara Shigo Da Kayayyaki Daga Iyakoki

Kwatsam Ta Zayyana Ƙa’Idoji Kafin Fara Shigo Da Kayayyaki Daga Iyakoki

98
0

Mukaddashin shugaban hukumar Kwastam na kasa Bashir
Adewale Adeniyi, ya zayyana ka’idojin da za a bi kafin a sake
bude iyakokin Nijeriya.

Bashir Adewale ya bayyana haka ne, yayin da ya ke yi wa jami’an hukumar jawabi yayin da ya kai ziyarar aiki a rundunar hukumar ta 1 da ke yankin Idiroko a jihar Ogun.

Ya ce hukumar za ta yi nazari a kan wasu tsare-tsaren ta, idan yankunan sun cigaba da bin doka da oda a kan abin da ya shafi shigo da kaya zuwa Nijeriya tare da fitar da su.

Adewale ya cigaba da cewa, daya daga cikin tsare-tsaren shi ne, sake yin nazari a kan tsarin tura man fetur zuwa gidajen saida mai, wadanda su ka kasance kilomita 20 daga iyakokin Nijeriya.

Ya ce akwai abubuwa da dama da alumomin su ke bukata, inda wasu daga cikin su sun fi karfin nauyin da gwamnatin tarayya ta dora wa hukumar, domin wasu tsare-tsaren nauyin mahukuntan Nijeriya ne.

Sai dai ya bada tabbacin cewa, su na kan aiki da sauran mahukuntan Nijeriya, kuma za su gabatar da bukata domin yin nazari a kan wadanan tsare-tsare.

Leave a Reply