Home Labaru Gwamnatin Najeriya Bata Fara Raba Kudi Ta e-Naira Ba – CBN

Gwamnatin Najeriya Bata Fara Raba Kudi Ta e-Naira Ba – CBN

75
0

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya karyata wani wani sauti da
ke yawo a kafafen sada zumunta a kan wani shirin gwamnati
na raba tallafi ga ‘yan kasa ta hanyar asusun E-Naira na
bankin.

Bankin na CBN, ya ce ba ya da masaniya a kan wannan sabon shiri da aka kago ta kafoffin sada zumunta, tare da yin kira ga ‘yan Nijeriya su yi taka-tsantsan kada wasu miyagu su cigaba da damfarar su ta wannan hanyar.

Wani matashi ya yi ikirarin cewa, shi ne jagoran aiwatar da tsarin asusun E-Naira na babban bankin a yankin Funtua na jihar Katsina a cikin wani sakon sauti, wanda ake ci-gaba da yadawa a kafoffin WhatsApp da Facebook da dai sauran su.

Mataimakin darakta kuma daya daga cikin jami’an da ke kula da aiwatar da tsarin E-Naira na Bankin CBN Muhammad Hamisu Musa, ya ce akasarin ababen da mutumin ya yi ikirari duk ba gaskiya ba ne.

Leave a Reply