Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda, ya amince da
nadin Abdullahi Garba Faskari a matsayin sakataren
gwamnatin jihar.
Babban mai taimaka wa Gwamnan a kafofin sadarwa na zamani Isah Miqdad ya wallafa sanarwar a shafin sa na Facebook, inda ya ce Abdullahi Garba Faskari ne zai canji Ahmed Musa Dangiwa, wanda zai zama Minista a gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A Tsakanin shekara ta 2011 da 2015 dai, Abdullahi Garba Faskari ne Mataimakin Gwamnan jihar Katsina a lokacin mulkin Ibrahim Shehu Shema.
Mutane da dama dai sun yi mamakin jin yadda tsohon Mataimakin Gwamnan zai zama sakatare.