Home Labaru Kwastam Ta Kama Kakin Soji A Iyakar Nijeriya Da Nijar

Kwastam Ta Kama Kakin Soji A Iyakar Nijeriya Da Nijar

106
0

Hukumar Kwastam mai kula da shiyyar Jihar Kaduna, ta ce a
cikin wata guda ta kama buhunhuna dauke da kakin sojoji da
kudin su ya kai naira miliyan 628.

Kwantuloran Kwastam na shiyyar jihar Kaduna Musa Jalo ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce, an kama kayan sojojin ne a tsakanin watan Maris zuwa Afrilu na shekara ta 2023, yayin da ake kokarin higo da su Nijeriya daga Jamhuriyar Nijar.

Ta ce yayin wani bincike da jami’an hukumar su ka yi, sun kama wata mota kirar Volkswagen Golf da wani dan kasar Nijar ke tukawa a kan hanyar Jibia zuwa Katsina.

Musa Jalo ya kara da cewa, bayan binciken da su ka yi, sun yi wa direban tambayoyi su ka gano cewa dan kasar Nijar ne, kuma ya na kan hanyar sa ta kai kayan ne ga wani da ba a gano ko wane ne ba a Katsina.

Ya ce tuni an mika kayayyakin da aka kama ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya domin ci-gaba da bincike tare da gurfanar da masu laifi a gaban kuliya.

Leave a Reply