Home Labaru Kiwon Lafiya Nijeriya Ce Ta Biyu A Yawan Mace-Macen Mata Masu Ciki

Nijeriya Ce Ta Biyu A Yawan Mace-Macen Mata Masu Ciki

1
0

Wani Rahoton Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ya ce, yanzu
Nijeriya ita ce ƙasa ta biyu a jerin ƙasashen da ke da yawan
mace-macen mata masu juna-biyu a fadin duniya.

Rahoton ya ce Nijeriya ke da kashi 29 daga cikin adadin dubu 290 na mace-macen mata masu jina-biyu da ake samu duk shekara, kuma ita ce kan gaba a faɗin duniya wajen aukuwar mutuwar jarirai da ƙananan yara.

Kasashen da ke fuskantar yawan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai da ƙananan yara, hukumar ta ce akwai Pakistan da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Habasha da Bangladesh da China da Indonesia da Afghanistan da kuma Tanzania.

Hukumar ta yi gargaɗin ne, duba da yadda al’amarin ya ke a halin yanzu, inda sama da ƙasashe 60 ciki har da Nijeriya na iya rasa cimma ƙudirin rage mace-macen mata masu juna- biyu da jarirai da ƙananan yara.

Sauran ɓangarorin da hukumar ta nuna damuwar ta a kai sun haɗa da ƙaruwar talauci da taɓarɓarewar jin-ƙai da ƙarancin kuɗi da ke ci-gaba da addabar ƙasashe a faɗin duniya.