Home Labaru Kotun Zabe: Atiku Da Namadi Sambo Sun Nemi Mambobin PDP Su Cure...

Kotun Zabe: Atiku Da Namadi Sambo Sun Nemi Mambobin PDP Su Cure Wuri 1

251
0

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar
da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo, sun ce
ba su cire rai da samun nasara a Kotun sauraren kararrakin
zabe ba.

Atiku Abubakar da Namadi Sambo, sun roki ‘yan jam’iyyar PDP su dunƙule wuri guda kuma kar su cire rai da samun nasara a Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban ƙasa.

Jiga-jigan biyu sun bayyana haka ne, a wajen liyafar da ƙungiyar gwamnonin PDP ta shirya wa zababbu da masu ci da gwamnonin PDP masu barin gado a birnin Abuja.

Haka kuma, Atiku Abubaka, ya buƙaci shugabannin jam’iyyar PDP su sake nazari, sannan su lalubo wasu dabarun da za su taimaka wa jam’iyyar ta sake mamaye siyasar Nijeriya.

A nasa bangaren, Namadi Sambo ya nuna damuwar sa a kan yawan kora da dakatar da ‘yan jam’iyyar PDP, inda ya yi kira ga muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa ya gaggauta shiga lamarin ya kuma bi duk matakan da ya kamata a cikin gida a sulhunta komai.

Leave a Reply