Home Home Kuskure: Hare-Haren Jiragen Sojin Najeriya Sun Kashe Yara Bakwai A Nijar

Kuskure: Hare-Haren Jiragen Sojin Najeriya Sun Kashe Yara Bakwai A Nijar

64
0
Sojojin Najeriya sun yi kuskuren kashe yara bakwai tare da jikkata wasu biyar a wani harin sama da suka kai a yankin Maradi na Jamhuriyyar Nijar, kamar yadda gwamman yankin ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa.

Gwamnan Maradi Chaibou Aboubacar, ya ce hare-haren sama da sojojin Najeriya suka kai ya rutsa da yara a ƙauyen Nachade a ranar Juma’a.

Gwamnan ya ce suna tunanin sojojin Najeriya sun yi kuskuren kisan yaran ne a ƙoƙarin kai wa ‘yan bindiga a yankunan kan iyaka hari.

Gwamnan Maradi ya ce lamarin ya shafi yara ne guda 12, kuma bakwai daga cikin sun mutu yayin da biyar suka jikkata.

A cewar gwamnan, harin ya rutsa da yaran ne suna cikin wasa yayin da iyayen su ke hidimar biki.

Sai dai har yanzun babu dai wata sanarwa daga rundunar sojin Najeriya game da al’amarin.