Home Home Portugal: Gobara Na Ci Gaba Da Cinye Dubban Motocin Alfarma Da Ke...

Portugal: Gobara Na Ci Gaba Da Cinye Dubban Motocin Alfarma Da Ke Cikin Wani Jirgin Ruwa

104
0
Masu aikin kashe gobara a Portugal sun ce har yanzu ba su iya kashe gobarar da ta tashi ba a wani makeken jirgin ruwa da ke ɗauke da dubban motocin alfarma wanda ke tafiya a cikin Tekun Atlantika.

Masu aikin kashe gobara a Portugal sun ce har yanzu ba su iya kashe gobarar da ta tashi ba a wani makeken jirgin ruwa da ke ɗauke da dubban motocin alfarma wanda ke tafiya a cikin Tekun Atlantika.

Jirigin mai suna Felicity Ace, na ɗauke da kusan motoci dubu huɗu da suka haɗa da motoci ƙirar Porsche da Audi da Bentley waɗanda ake hanyar kai su Amurka daga Jamus.

Tuni aka ceto ma’aikatan jirgin ruwan 22, Sai dai wani ma’aikaci a tashar ruwa da ke wani tsibiri ya bayana cewa ruwan da ke cikin batiran wasu motocin ne ya sa wutar ke ci gaba da ci.

Ya ce wutar ba ta kai ga tankin mai na jirgin ba, Haka kuma ya bayyana cewa kashe irin wannan wutar na buƙatar kayan aiki na musamman sakamakon ruwan kashe gobara na gargajiya ba zai iya kashe wutar da ruwan batir ya zama makamashin ta ba.