Home Home Luguden Wuta: Sojojin Najeriya Sun Kashe Kwamandojin ISWAP A Sambisa

Luguden Wuta: Sojojin Najeriya Sun Kashe Kwamandojin ISWAP A Sambisa

434
0
Rahotanni sun ce sojojin Najeriya sun halaka wasu kwamandojin Iswap a Sambisa ciki har da wanda ake kira Amir Buba Danfulani wanda ake zargin ya shigar da fulani makiyaya ƙungiyar.

Rahotanni sun ce sojojin Najeriya sun halaka wasu kwamandojin Iswap a Sambisa ciki har da wanda ake kira Amir Buba Danfulani wanda ake zargin ya shigar da fulani makiyaya ƙungiyar.

A cikin rahoton da ta fitar, jaridar PRNigeria ta ce an yi wa mayaƙan ne luguden wuta ta sama a wasu sansanonin su da kuma dajin Sambisa.

Rahotannin sun ce an yi wa mayaƙan ne ruwan rokoki a Tumbun Kaiyowa da kuma Tumbun Allura, tare da kashe mayaƙan.

A cewar PRNigeria Kwamandojin Iswap da aka kashe sun hada da Musa Amir Jaish da Mahd Maluma da Abu-Ubaida da Abu-Hamza da kuma Abu-Nura umarun Leni,.

Sai dai babu wata sanarwa kawo yanzu daga rundunar sojin Najeriya da ke tabbatar da al’amarin.

Leave a Reply